15 Satumba 2025 - 10:29
Source: ABNA24
Yadda Ta Kaya A Majalissar Iran Kan Batun Yarjejeniyar Kwanan Nan

Tare da gabatowar wa’adin aiwatar da takunkuman kasashen turai kan lamarin nukiliyar Iran, yanayin siyasa da diflomasiyya da ke tattare da wannan lamari ya kara zafafa fiye da kowane lokaci. Daya daga cikin muhimman sharuddan Turai don hana kunna wannan takunkuman shi ne kulla yarjejeniyar Iran da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, wadda aka cimma a baya-bayan nan.

Kamfanin dillancin labarai na AhlulBaiti: bias nakaltowa daga jaridar cewa: Tare da gabatowar wa’adin aiwatar da takunkuman kasashen turai kan lamarin nukiliyar Iran, yanayin siyasa da diflomasiyya da ke tattare da wannan lamari ya kara zafafa fiye da kowane lokaci. Daya daga cikin muhimman sharuddan Turai don hana kunna wannan takunkuman shi ne kulla yarjejeniyar Iran da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, wadda aka cimma a baya-bayan nan.

Duk da cewa an tantance yarjejeniyar ne bisa tsarin manyan muradun kasar da amincewar doka daga gwamnati da kuma komitin tsaron kasar, amma ta fuskanci kakkausar suka daga wasu jiga-jigan ‘yan majalissar da wakilan majalisar dokoki. A halin da ake ciki, wani muhimmin sharadi na gaba da kasashen Turai suka sanya shine, wato cimma yarjejeniya da Amurka, yana ci gaba da kasancewa cikin yanayi na rashin tabbas, kuma babu labarin tattaunawa a hukumance ko ci gaba mai ma'ana a wannan fanni, don haka shirin nukiliyar Iran yana cikin mawuyacin hali. Duk da cewa kamfanin dillancin labaran kasar Rasha TASS ya yi ikirarin cewa ana ci gaba da tattaunawa a kaikaice tsakanin Tehran da Washington ta hanyar masu shiga tsakani, Iran ta bayyana karara cewa za ta shirya kanta ne kawai don tattaunawar diflomasiyya idan har Amurka ta shirya yin tataunawa bisa mutunta juna. Iran ta jaddada cewa dole ne a mutunta hakkokinta da muradunta. Wannan matsayi yana nuna zurfin rashin yarda da fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu. A halin yanzu, maganganun Wendy Sherman, tsohuwar mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka, suna da ban mamaki. Ta yi nuni da cewa har yanzu shirin nukiliyar Iran yana nan daram kuma barnar da aka yi masa bata shafi gaba dayansa ba, tana fatan za a iya maido da diflomasiyya tsakanin Iran Da Amurka.

Amma a Iran, zartar da yarjejeniya da hukumar ta IAEA ta zama wani al'amari mai sarkakiya da muhimmanci. Bayan sanar da yarjejeniyar, kwamitin tsaron kasa da manufofin harkokin waje na majalisar ya gudanar da wani taron gaggawa tare da halartar ministan harkokin wajen kasar Abbas Arakchi domin nazarin ma'auni na yarjejeniyara da aka rattabawa hannu. Araqchi, yayin da yake bayyana tsarin tattaunawar da aka fara da kwararru a lokuta da dama, kuma daga karshe ya haifar da fahimtar juna a wannan yarjejeniyar a wata ganawa kai tsaye da babban daraktan hukumar ta IAEA a birnin Alkahira, ya jaddada cewa Turai ba ta da hakki a dokance na aiwatar da takunkumai da za ta yi amfani da shi wajen kuntatawa Iran, kuma duk wani mataki da zata dauka a wannan hanya ana daukarsa a matsayin ba bisa doka ba. Har ila yau ya ce, hadin gwiwar aikin Iran da hukumar IAEA, an zartar da shi ne bayan amincewar majalisar dokoki da kuma la'akari da sabbin yanayin tsaro, dole ne a aiwatar da shi bisa wani sabon tsari, kuma za a gudanar da duk wani bincike ne kawai bisa tsarin doka da amincewar kwamitin koli na tsaron kasa.

To sai dai kuma, 'yan majalisar da suka amince da rahoton na ministan harkokin wajen kasar, sun jaddada bukatar aiwatar da cikakken dokar dakatar da hadin gwiwa da hukumar ta IAEA, da kuma kiyaye hakkin Iran. Dan Majalisar Dashtestan Ebrahim Rezaei ya yi kira da a fayyace cikakkun bayanai game da yarjejeniyar da kuma kare lafiyar masana kimiyyar nukiliya, amma wasu masu tsatsauran ra'ayi, irin su Kamran Ghazanfari da Hamid Rasaei, sun soki yarjejeniyar tare da yin kira da a buga cikakken bayanin yarjejeniyar da kuma nuna gaskiya; Ghazanfari ya yi barazanar tsige Ministan Harkokin Wajen, kuma Rasaei ya yi gargadin cewa tsarin na yanzu zai iya haifar da maimaita abun da ya faru a yarjejeniyar JCPOA.

Dangane da haka, sakatariyar komitin tsaron kasar ta fitar da wata sanarwa da ta tabbatar da cewa nassin yarjejeniyar ya yi daidai da amincewar kwamitin nukiliyar majalisar. Wannan kwamiti ya ƙunshi manyan jami'ai daga cibiyoyin da abin ya shafa kuma yana da ikon yanke shawara game da hakan. Sanarwar ta jaddada cewa, dangane da kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran, za ta mika rahotonta ga hukumar ta IAEA bayan tabbatar da tsaro da kiyayewa da kuma samun ra'ayin komitin tsaron kasar, kuma duk wani mataki na zahiri dole ne ya zama majalisar ta amince da shi. An kuma sanar da cewa, idan aka dauki wani mataki na nuna adawa, ciki har da maido da kudurorin kwamitin sulhu, nan take za a dakatar da aiwatar da yarjejeniyar.

Wadannan matsayi na nuni da cewa, a matakin da ya dace na tsaro, Iran tana son yin hulda da hukumar bisa sharadi da basira, yayin da a lokaci guda kuma ta zayyana jajayen layukan gaba da gaba da kasashen yamma. Duk da haka, yanayin wannan yarjejeniya bai bude kofar dabarun siyasa na dogon lokaci ba ko kuma cikakken ja da baya, sai dai samar da "hanyar tsaro ta siyasa" da aka tsara don sayen lokaci da rage tashin hankali.

Duk da haka, cikas da barazanar da ke fuskantar wannan yarjejeniya suna da yawa kuma masu rikitarwa ne. A cikin gida, akwai adawa daga wani sashe na majalisar dokoki da matsin lamba na siyasa na iya haifar da babban kalubale ga tsarin hadin gwiwa. Har ila yau, karuwar hare-haren da Isra'ila ke kai wa kan cibiyoyin nukiliyar Iran a baya-bayan nan ya tsananta rashin amincewa da hukumar, kuma duk wani sabon matakin soji na iya sanya wannan yarjejeniya ta yi tasiri. A gefe guda kuma, haɗarin Turai ko Amurka na aiwatar da takunkumai, duk da rashin tabbas na doka, barazanar siyasa ce da za ta iya dakatarwa ko mayar da JCPOA maras ma'ana. Bugu da kari, karuwar matsin lamba da takunkumin siyasa zai yi tasiri kai tsaye kan harkokin musayar kudaden waje da kasuwannin zuba jari da kuma daidaita tattalin arzikin kasar; batun da hatta ministan harkokin wajen kasar bai yi biris da shi ba, duk da raguwar karin gishiri a lamarin.

Duk da haka, yarjewa da sa hannu a yarjejeniyar kwanan nan tana ba da dama; ciki har da samar da wata hanya ta kulawa da tashin hankali tare da Hukumar da kuma hana kai karar zuwa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, samar da yiwuwar tattaunawa ta fasaha da za ta iya zama garkuwa ga matsin lamba na siyasa, da kuma kafa rawar da komitin tsaron kasa na koli a cikin jagorancin shirin nukiliyar da ke karfafa haɗin kai tsakanin cibiyoyin da suka dace.

A ƙarshe, makomar wannan tattaunawa ya dogara ne da ikon gwamnati don tafiyar da matsalolin cikin gida da yanayin yanki da na duniya. Idan aka ci gaba da yin hadin gwiwa tare da hukumar bisa sharadi, kuma aka dakatar da aiwatar da sabbin Takunkuman, Iran za ta samu damar gudanar da manufofinta na nukiliya da tattalin arziki yadda ya kamata. Duk da haka, idan hargitsi ya karu kuma kasashen yamma ko Isra'ila suka dauki matakin kiyayya, kasar za ta fuskanci wahalhalun siyasa da tattalin arziki. Don haka ya kamata a yi la'akari da yarjejeniyar da ke tsakanin Iran da hukumar a matsayin farkon wani sabon salo mai sarkakiya a tafarkin makaman nukiliya; Matakin da ba kawai rubutun yarjejeniyar ba ne, har ma da manufofin cikin gida da ci gaban yanki na tabbatar da makomarsa. A cikin wannan yanayi, duk wani ci gaba na buƙatar daidaito tsakanin muradun tsaron ƙasa, matsin lamba na cikin gida, da hulɗar ƙasashen duniya.

Wahida KarimiVahida Karimi: Sakatariyar Sashen Siyasa na Jaridar Shargh

Your Comment

You are replying to: .
captcha